Hausawa sunce koda naka Kaso na kwarai.
Marubuciyar (Nblog) Kuma Blogger Ta Zamfara tace
"Jama'an Zamfara mu sani bawai jam'iya ke aiwatar da aiki ba Dan takara ke aiwatar da aiki.
Don haka nake Kira da dukkanni mutanen Zamfara da KEWAYE da yakamata muyi tunani akan mutumin da zai ceto mu cikin halin da muke ciki a jahar Zamfara, shin munajin dadin yanda ake cin zarafin mu a wulakanta mu da iyalen mu da matan mu ana Masu fyade da yayanmu, akwashe dukiyoyin mu a rabamu da muhalan mu.
Ya kamata ya yan uwa Maza da mata mu farka, kuma mu sani fa inda akuyar gaba Tasha ruwa nan ta baya Kesha, mun gaji da mulkin gado DOMIN Mulki ba sarauta bane da za ace don kayi sai danka yayi anaso amaidamu bayi a jahar Zamfara.
Don haka nake cewa mu zabi mutum mai cancanta, tausayi, imani.
Alhaji (Dr.) Sani Abdullahi Shinkafi (Wanban Shinkafi) na jam'iyar APGA a matsayin gomnan mu domin manufofin shi na alheri, munsani yazone domin yacetomu daga halin da muke ciki, shi bayazo satar dukiyar mu bane kamar sauran domin ba abinda yake nema da Allah bai bashiba, ya ku yan uwa na zamfarawa mu kauda naira dubu daya, dubu biyu na ranar zabe mu zabi wanbai gaskiya dokin karfe 2019"
Domin ci gaban Al'ummar mu gaba daya
Sako daga:- Marubuciyar NBlog
0 comments:
Post a Comment