Dr Sani Abdullahi Shinkafi, Dan takarar kujerar gwamnan jahar Zamfara ta jam'iyar APGA ya bayyana cewa tsayawar shi takara yazamo wajibi akanshi domin talakawan jahar sa ke Kira sa domin ya ceto su.
Dr Sani Abdullahi Shinkafi (Wanban Shinkafi) yace
"Banyi niyyar tsayawa takarar gwamna ba 2019 dole ce tasa. Sanadiyyar ganin halin da mutanen zamfara suka shiga, Na rashin tsaro, matan aure sunkoma zawarawa, ankashe mazajensu, yara sunkoma marayu Ankashe iyayensu, an anshe dukiyoyinsu , suna yawo cikin garuruwa suna bara, amma gwamnati ta kasa tallafa masu, shekara takwas baa dauki matasa aikiba, babu ingantaccen ilimi, jahar zamfara takoma baya awurin tattalin arziki, an sace kudin jaha. Ganin wannan shiyasa Naga yazama wajibi inyi takarar gwamna domin qwatoma Al ummah haqqoqansu. Asamar da tsaro, aikin yi ga matasa , farfado da tattalin arzikin jaha, dakuma Samar da ingantaccen ilimi."
0 comments:
Post a Comment