Alhaji Dr Sani Abdullahi Shinkafi (Wanban Shinkafi) wanda aka fi sani da Wanbai, ya sha alwashin cewa idan ya zama Gwamnan Jihar Zamfara zai nuna kyakkyawan shugabancin siyasa wajen ciyar da jihar gaba ta hanyoyi da dama cikin lumana ba tare da cin zarafin kowa ba.
Ya bayyana haka ne jim kadan da sayen fom tsayawa takarar Gwamna a karkashin Jam’iyyar APGA, inda ya ce ya san bukatun mutanen kauyuka da biranen jihar,
Wanban Shinkafi Yace;
"Karcen ta'addanci ya zaizo jihar Zamfara idan nazama gwamna, domin zanyi Aki 24/7 da hukumar tsaro domin ganin karshen kashe kashe da sace sace a jihar Zamfara da KEWAYE"
“Na yi aiki da gwagwarmaya, inda ta sa na san mutum a matsayin halitta mai daraja, ba abin wulakantawa ba, kamar yadda wadansu ke yi bayan an zabe su, sun hau gadon mulki,” inji shi.
Ya kara da cewa, zai samar da tsarin bunkasa tattalin arziki da inganta ababen jin dadin rayuwa da kyautata zaman lafiya da daraja hakkin dan Adam da samar wa jama’a aikin yi da kula da kudin jihar. Sai ya kudiri niyyar jin ra’ayin jama’a kafin aiwatar da manyan ayyuka.
Yace;
“Na yi takara 2015 domin neman zama Gwamnan Jihar Zamfara, kuma ina jin dadin yadda jama’a a yanzu suka fara fahimtar mulkin farar hula da wayewar siyasar yin mutum ba jam’iyya ba,” inji shi"
0 comments:
Post a Comment